TARIHIN DAN WASA CRISTIANO RONALDO A TAKAICE ! - Agajahub publisher

TARIHIN DAN WASA CRISTIANO RONALDO A TAKAICE !

CIKAKKEN TARIHIN DAN WASA CRISTIANO RONALDO A TAKAICE !


Cikakken Sunasa Shine Cristiano Ronaldo Dos Santos Aveiro,

An Haife Shi Ranar 5 Ga Watan Fabarairu 1985 A Birnin

Mandeira Ta Kasar PORTUGAL.

Ronaldo Ya Fara Taka Leda Ne A Kungiyar Kwallan Kafa Ta

SPORTING CP Ta Kasar Portugal, Kafin Ya Tsallaka Kungiyar

Kwallan Kafa Ta Manchester United A Shekara Ta 2003, A

Lokacin Yana Dan Shekara 18.

Dan Wasan Gaba Wato Winger/Forward/Striker, Sannan Shine

Captain Din Kungiyar Kwallan Kafa Ta Kasar Portugal.

Manchester United Ta Siyi Dan Wasan A Shekarar 2003 Daga

Kungiyar Kwallan Kafa Ta SPORTING CP Ta Kasar Portugal.

Cristiano Ronaldo Ya Fara Buga Premier League Ne A Ranar 16

Ga Watan August 2003, A Wasan Da Manchester United Din Ta

Samu Nasarar Casa Kungiyar Kwallan Kafa Ta BOLTON

WANDERERS Daci 4:0 Da Nema.

Kwallan Cristiano Ronaldo Ta Farko A Manchester United Yaci

Ta Ne Da Free Kick, A Wasan Da Suka Samu Nasara Daci 3:0

Da Nema Akan Kungiyar Kwallan Kafa Ta PORTMOUTH.

Red Card Dinsa Na Farko A Manchester United Shine Wasansu

Da Aston Villa A Kakar Wasa Ta 2003/04.

Ronaldo Ya Kafa Tarihi A Manchester United, Inda Shine Dan

Wasan Da Ya Ciwa Manchester United Kwallanta Na

# DUBU1000 A Premier League, A Wasan Da Suka Sha Kashi A

Hannun Kungiyar Kwallan Kafa Ta Midlesbrough Daci 4:1 A

Ranar 29 Ga Watan October.

KADAN DAGA CIKIN NASARORIN DA YA SAMU

1) Portugal Ta Bayyana Shi A Matsayin Dan Wasanta Mafi Hazaka A Tarihi Tun Fara kwallo ta Portugal 2) ya lashe kyautar Ballon d"or sau 53) Ya Lashe Kwafa Kwafai 10 A Manchester United4) Ya Lashe Kwafa Kwafai 15 A Real Madrid5) Ya Zira Kwallaye 815

6) Yayi Assists 273

7) Ya Buga Wasanni 1100

Matarsa 1 'ya'yansa 4


Cristiano Ronaldo ya koma Manchester United shekaru 12 bayan barin kungiyar - amma wanne irin dan wasa ne yakoma gasar Premier a yanzu?

Dan wasan ya ci kwallo 551, tun da ya bar Old Trafford ya

koma Real Madrid a 2009, ya ci Champions hudu tare da

kyautar Ballons d'Or ita ma guda hudu, ya ci La Liga hudu da

kuma dan wasan da ya fi zura kwallaye da yawa a gasar.

Yayin da ya kai shekara 36, ta tabbata dan wasa ya wuce

ganiyarsa, amma kididdiga ta nuna har yanzu yana cikin

taurarin nahiyar Turai wadanda suka fi zura kwallo.

Ta yaya za mu iya kwatanta Ronaldo da kuma kalla a baya da

na yanzu?

Kwallaye...

Yawan cin kwallayen Ronaldo ya ragu tun bayan da ya ci wa

Real Madrid kwallo 40 a kaka uku cikin biyar. A 2014-15 ya ci

kwallo 61 a wasa 54 da ya buga.

Duk da za a iya cewa nasararsa ba ta yi nisa ba Juventus,

amma dai ya ci kwallo 101 cikin wasanni 134 da ya buga a

duka gasa.

Idan muka kwatanta lokacin da

Ronaldo yana matashinsa ya ci

kwallo 118 a wasa 292 a kaka

shida da ya buga a United.

Kwallaye 29 da ya ci su ne suka

ishe shi ya zama ya lashe

takalmin zinare, ya kara a kan

wanda ya ci a Premier a (2008)

da na La Liga a (2011, 2014 da

kuma 2015).

Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Welcome to Agajahub publisher coment section please do not spam in this blog