Abubuwa 7 da cin kwai yake samar wa yara ‘yan kasa da shekaru biyar - Agajahub publisher

Abubuwa 7 da cin kwai yake samar wa yara ‘yan kasa da shekaru biyar

Abubuwa 7 da cin kwai yake samar wa yara ‘yan kasa da shekaru biyarBa yara kwai a lokacin da suke tasowa na da matukar amfani domin yana inganta girman jikin yaran saboda sinadarorin da kwan ke dauke da shi.

🥚🥚🥚

Bayanai na kwararru ya nuna cewa kwai na dauke da sinadarorin Vitamin A, B12, D, B6 wanda ke taimakawa wajen kara karfin garkuwan jiki yara musamman ‘yan kasa da shekaru 5.

🥚1. Dafaffen kwai na bude kwakwalwan yaro.

🥚2. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin ‘lutein’ and ‘zeaxanthin’ wanda ke kara lafiyar idanuwar yaro.

🥚3. Dafaffen kwai na kara karfin kashi a jikin yara kanana domin yana dauke da sinadarin Vitamin D.

🥚4. Dafaffen kwai na dauke da sinadarorin leucine, phenylalanine, histidine, isoleucine, lycine, methionine, threonine, tryptophan da valine wanda suke taimakawa wajen gina jikin yaro da kuma kara masa jini.

🥚5. Dafaffen kwai na kara girman kunba da gashin kan yara.

🥚6. Omega-3 da ke cikin dafaffen kwai na taimakawa wajen bude kwakwalwar yaro kuma zai yi sauran gane abubuwa.

🥚7. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin Iron da ke taimakawa wajen samar da issashen jini a jikin yaro Wanda rashin shi yakan sa aga yaro na kumbura.


Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Welcome to Agajahub publisher coment section please do not spam in this blog